Gwamnatin Najeriya za ta rage farashin man fetir zuwa Naira 85 daga ranar daya ga watan Janairun sabuwar shekarar 2016 da zamu shiga.Farashin zai sauka daga Naira 87 zuwa 85 kamar yadda Ministan kasa na man fetir Emmanuel Kachikwu ya tabbatar wa manema labarai a garin Fatakwal
Ministan yace tun a ranar Alhamis ne ya sanya hannu kan matakin, kuma zuwa 1 ga watan Janairu tsarin zai fara aiki.
Tuntuni ne ake hasashen gwamnatin Najeriya zata rage farashin fetir saboda faduwar danyen mai a kasuwannin duniya.
Najeriya za ta rage farashin Man fetir zuwa 85
Reviewed by Musa Abdullahi
on
16:03
Rating:
No comments: