Ina kara godiya ga masu karatu wadanda a koda yaushe suke nuna mani kwarin gwiwa kan yadda muke gabatar da batutuwa a wannan shafi. Hakika, ilmi ko yaya yake ba abin rainawa ba ne, ina jin dadi matuka kanyadda aka samar da wannan kafar da ‘yan’uwana mata suke amfana domin samun ci gaba a cikin zamantakewarmu.
Haka kuma, ba zan manta da kwarin gwiwa da goyon bayan da nake ta samu daga wajen maigidana ba, wanda shi ma dan jarida ne. Hakan ya kara ba ni damar ci gaba da wannan shafi mai yawan kaluaale
A duk inda ake zancen mace, gyara jiki shi ne abin da ake tinkaho da shi. AYau na shhigo muku ne da wasu karin sirrukan da za su taimaka muku matayan’uwana.
Bari mu fara da tuna wa juna cewa namiji a kowane hali, abin tattali ne. Don haka, ya kamata a kullum mu rikasanin cewa namiji fa dan goyo ne ga wadda ta iya. Ku girmama mazajenku ko kwa sami Aljannar Ubangijinku cikin sauki
Ni'ima Adon Mata
Dalilai da dama sun kasance manuniya ga zancen da muka faro a sama, wato tun da mun yarda cewa namiji dai abin tattali ne, to kuma yana da kyau mu fahimci irin tattalin da ya kamace shi. Akwai hidindimun da mace za ta rika yi wa mijinta domina gudu tare, a tsira tare. Addini ya hukunta cewar babu bambaci a tserenimani tsakanin namiji da mace. Ma’ana, don ya kasance mace tana karkashin namiji, bai zama kuma cewa a kullum a baya take ba. A’a, ana nufin ta kasance abokiyar tafiyarsa ne don ya samu saukin rayuwa. Daya daga cikin ababen da zasu amfani tafiyar namiji da mace shi ne tattalin kai, wanda mace ya kamata ta rika yi wa mijinta.
Wannan tattalin da ake magana a nan, ya shafi gyara jiki, nemankarin ni’ima domin saukaka ibadar aure da sauransu. A harkar gyaran jiki, babu macen da ta ba ta san amfanin: Lalle da kayayyakinsa ba.
Bari mu duba yadda ya kamata a yi amfani da wannan sinadarin:
Abubuwan da za a tanada sun hada da:
(1) Lalle
(2) Kwaiduwar kwai (guda uku)
(3) Manja (Cokali uku)
(4) Cocumber
(5) Kur-kur
Idan kin sami wadannan kayan da muka lissafa, ki hada su waje daya, ki kwaba, sai dai Cocumber kadai za ki markada, ki tace ruwan, sannan ki zuba a kai. Bayan nan, sai ki kwaba sai ya hadi sosai yadda ake bukata.
Kiba shi kamar minti goma ko ashirin, ya tsumu, sannan ki shafa a jikinki, ki ba shi awa guda sannan ki yi wanka da sabulun Ghana ko na Sabulun Salo
Alal hakika, wannan yana aya daga cikin sinadaran da ke gaggauta gyaran jiki, gami da kara wa mace martaba, ni’ima da jin dadin rayuwartaa dakin miji.
Nazari Akan Ayaba
yaba na daya daga cikin kayan marmari da ke aljannah, kuma Allah (S.W.T. ) ya yiwa bayinsa muminai alkawari da ita, fadar Allah madaukakin sarki, a cikin suratul waki’ah (56:27-30)
Wani binciken da likitocin muslunci suka yi akan kasar Australia (7-January, 1991), sun nuna cewa tana da matukar amfani ga dan Adam.

Good post, Musa.
ReplyDeleteKaranta: Sirrikan Mallakar Miji a musulince na har abada.