Random Posts

Technology

test

An abkawa Musulmi a Masallaci a Faransa

Wasu gungun masu zanga-zanga a Faransa sun abkawa wani masallaci tare da Kona Al Qur’ani mai tsalki a yankin Ajacci.Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Juma’a bayan an kashe wasu ‘Yan Sanda da jami’an kashe gobara guda biyu a yankin Jardins de L'Empereur.

Mutane sama da 150 suka hada gangamidomin nuna goyon baya ga ‘Yan sanda bayan kashe jami’ansu guda biyu.

Amma daga baya kuma wasu daga cikin masu zanga-zangar suka abkawa Masallaci suna fadin Larabawa su fice kasarsu tare da farfasa kofa da tagogin masallacin da kuma kona wani sashe na Al Qur’ani mai tsarki.

Gwamnatin Faransa dai ta yi allawadai daal’amarin wanda ta danganta a matsayin nuna wariya da kyamar baki.

Jam’iyyar ‘Yan kishin kasa ce ta Marine Le Pen mai adawa da bakin haure ta lashe zaben kananan hukumomi da aka gudanar a yankin Corsica inda aka kai wa musulmin harin a jiya.

An abkawa Musulmi a Masallaci a Faransa An abkawa Musulmi a Masallaci a Faransa Reviewed by Musa Abdullahi on 15:50 Rating: 5

No comments:

Blogs We Read

Breaking

Translate

Gallery

Powered by Blogger.